
Kungiyar Matasan Yarbawa, (YYSA) tace bata amince da kiran da kungiyar dattawan Yarbawan ta yi ba na cewa a tsige shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda yaudarar ‘yan Najeriya.
Shugaban kungiyar, Olalekan Hammed ne ya fitar da sanarwar ranar Lahadi inda yace zargin da akewa shugaba Tinubu na baiwa kamfanin Mr. Gilbert Chagoury aikin gina titin Legas zuwa Calabar wanda ke da alaka dashi ba gaskiya bane.
Yace kamfanin na da tarihin yin ayyuka masu kyau.
Yace kiran a tsige shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu cike yake da siyasa sannan zargin da ake masa bashi da tushe ballantana makama.
Sannan yacw shi Tinubu yana duba cancanta ne kamin ya bayar da aiki.