Friday, December 5
Shadow

HAJJIN 2025: Yariman Saudiyya ya yi kira da kakkausar murya da a dakatar da kìsàn kìyàshì da ake wa Fàlàsɗìnàwà

Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya kira ga al’ummar duniya da a dauki matakin dakatar da hare-haren da ake kai wa Gaza yana mai jaddada cewa akwai buƙatar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin ta hanyar bin ka’idojin na duniya.

Yariman Saudiyya ne ya yi wannan kira ga al’ummar duniya domin kawo karshen fadan da ake yi a Gaza.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa ( NAN) ya rawaito sarki Salman na bayyana haka cikin saƙon da ya gabatar na taron shekara a lokacin a Muna a ranar Asabar.

Ya jaddada cewa daukar mataki domin kare rayukan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da kuma samar da yanayi na zaman lafiya da walwalar ga Falasɗinawa muhimmin abu ne.

Karanta Wannan  China za ta haramta tsawwala sadakin aure da bikin 'almubazzaranci'

Ya ce, “wannan roƙi na nuna yadda kasar Saudiyya ta himmatu wajen kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa da samar da kwanciyar hankali a yankin.”

Ya kuma bayyana cewa Saudiyya za ta cigaba da hidimta wa Musulmi musamman a a lokacin Hajji da kuma jaddada ƙoƙarin kasar na saukaka gudanar da ibada.

Sannan ya jaddada muhimmancin tsaro da kwanciyar hankali a kasashen Musulmi a duniya.

Yarima mai jiran gado ya jaddada buƙatar shigowar ƙasashen duniya na sa hannu wajen kawo karshen hare-haren Isra’ila a kan Falasɗinawa.

Taron cin abincin ya samu halartar mutane da suka haɗa da shugabannin kasashen Mauritania, Mohamed Ghazouani, da shugaban Maldives, Mohamed Muizzu.

Karanta Wannan  Nan da shekarar 2027 za'a samu karin Talakawa a Najeriya>>Inji Bankin Duniya

Ministan aikin Hajji da Umrah, Tawfiq Al-Rabiah, ya bayyana irin cigaban da aka samu a lokacin Hajjin bana wanda ya haɗa da samar da sabon karsashi da ayyuka more rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *