Friday, December 5
Shadow

Shugaba Tinubu zai karrama wasu ‘yan Majalisa a ranar Dimokradiyya

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai karrama wasu ‘yan majalisar tarayya saboda ranar Dimokradiyya.

Tuni gwamnatin tarayya ta sanar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar hutu dan ranar Dimokradiyya.

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai yi amfani da wannan dama dan karrama wasu sanatoci da ‘yan majalisar wakilai.

Shugaba Tinubu zai gabatar da jawabi ga zaman ‘yan majalisar na hadaka tsakanin ‘yan majalisar Wakilai da Sanatoci da misalin karfe 12 na ranar 12 ga watan.

Kuma zai yi maganane akan cikar Najeriya shekaru 26 da Dimokradiyya ba tare da yin juyin mulki ba, kamar yanda kakakin majalisar, Akin Rotimi ya bayyanar.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya koma jihar Kebbi da zama kamar yanda shugaba Tinubu ya umarceshi

Ko da a shekarar 2024 ma dai, shugaba Tinubu ya baiwa kakakin majalisar Dattijai, Godswill Akpabio da takwaransa na majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da mataimakin kakakin majalisar Dattijai, Sanata Barau Jibrin da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu lambobin girmamawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *