
Tsaffin magoya bayan Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, sun koma jam’iyyar NNPP daga APC.
Sumaila wanda aka zaba a jam’iyyar NNPC ya watsar da jam’iyyar inda ya koma APC shi da mutanen mazabarsa a watannin da suka gabata.
Saidai magoya bayan nasa a yanzu sun barshi inda suka koma jam’iyyar APC bisa jagorancin Jamilu Zamba inda suka ce ya ci amanarsu.
Masu komawa NNPP din sun fito daga kananan hukumomin Albasu da Sumaila . Akwai kuma wadanda suka fito daga Bunkure da Tofa da sauransu.
Da yake karbarsu a gidansa dake Titin Miler Kano, Kwankwaso ya bayyana cewa ana musu maraba kuma za’a musu adalci a jam’iyyar NNPP.