Friday, December 5
Shadow

An kama wannan mutumin ya saci kwalayen sigari guda 9 daga wani Super Market wanda darajarsu ta kai Naira Dubu 90

Rahotanni sun bayyana cewa, jami’an tsaro a jihar Legas karkashin rundunar RRS dake Falomo a Ikoyi sun kama wani mutum da kwalayen sigari guda 9 da ya sata daga wani babban shagon da ake cewa, Super Market.

An kiyas ta cewa darajar kwalayen sigarin da ya sata zasu kai Naira Dubu 90.

Hukumar ‘yansandan tace ta kama wanda ake zarginne da misalin karfe 5:30 pm na yammacin ranar Labadi.

Hukumar ‘yansandan tace kowane kwalin sigari ana sayar dashi akan Naira dubu 10 wanda jimulla kudin sigarin da ya sata Naira dubu 90 kenan.

Sunce Tuni suka mikashi ga hukumar ‘yansanda ta Falomo.

Karanta Wannan  Ba matsala bane dan siyasar Najeriya ta koma Jam'iyya daya kawai, Adalcin Shugaba Tinubu ne yake kawo 'yan siyasa APC>>Inji Ganduje

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *