
Ministan Ayyuka, David Umahi ya bayyana cewa, bayan Allah sai Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a wajensa.
Ya bayyana hakane a yayin ganawa da manema labarai a Abakaliki yayin da yake bayyana irin jinjina da amincin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bashi.
Yace yabon da shugabab kasa, Bola Ahmad Tinubu ya masa yafi mai a bashi Dala Tiriliyan daya.
Yace kuma a kullun yana fada idan har ya dora iyalinsa ko danginsa a sama da Allah ko Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu to kada Allah ya biya masa bukatunsa.