Friday, December 5
Shadow

Bèllò Tùrjì ya ƙaƙaba harajin Naira Miliyan 50 kan manoma a Zamfara da Neja

Bello Turji ya ƙaƙaba harajin Naira Miliyan 50 kan manoma a Zamfara da Neja

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Mazauna wasu yankunan da dama a jihohin Zamfara da Neja sun sake shiga wani mawuyacin hali, bayan da sanannen jagoran ƴan bindiga, Bello Turji, ya bukaci a biya naira miliyan 50 kafin a basu damar fara aikin noma na bana.

LEADERSHIP ta rawaito cewa wannan bukatar ta fito fili ne ta bakin wani mai nazarin tsaro mai suna Bakatsine, wanda ya wallafa bayani a shafinsa na X , inda ya bayyana cewa shugaban ƴan bindigar ya kakaba kudin a matsayin sharadi na samun zaman lafiya.

A cewarsa, “An bada rahoton cewa shugaban ƴan bindiga, Bello Turji, yana bukatar naira miliyan 50 daga mazauna Tsalaken Gulbi daga kauyen Fakai, Karamar Hukumar Shinkafi, Jihar Zamfara, har zuwa Qaya da ke kusa da iyakar Jihar Neja, kafin ya barsu su yi noma a kakar bana,” in ji Bakatsine.

Karanta Wannan  Jahilaine ke shugabantar Najeriya a yanzu>>Malam Nasiru Ahmad El-Rufai

Bello Turji na daga cikin fitattun shugabannin ƴan bindiga da aka dade ana danganta su da hare-hare masu muni, garkuwa da mutane da kuma haramtaccen karbar haraji daga kauyuka.

Rahotanni sun ce ikon Turji ya mamaye wasu sassa na jihohin Zamfara, Sakkwato da Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *