
Kasar Amurka ta bayar da umarnin kwashe ma’aikatan ta dake ofishin jakadancinta na kasar Iraqi inda ta bayyana cewa akwai fargabar tsaro.
Hakanan rahotanni sun ce Amurkar ta na kwashe wakilanta daga kasar UAE
Ana tsammanin haka shirine na Afkawa kasar Ìràn da yaki saboda hanata mallakar makamin kare dangi.
Kasar Iran tace muddin Amurka ko Israyla suka kai mata hari, zata tabbatar ta kaiwa kadarorin kasar Amurkar dake yankin Gabas ta tsakiya hari.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, ba zasu bar Iran ta mallaki makamin kare dangi ba.
Rahotanni sun ce kasar Iran ta ki baiwa Amurka hadin kai a tattaunawar neman sulhu dan karta mallaki makamin kare dangi.