
Kungiyar yarbawa magoya bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu me suna (NOYAT) sun yiwa shugaban kasar Alkawarin samar masa da kuri’u Miliyan 10.
Kungiyar a shekara 2022 ta shirya taro na musaman kan goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a jihar Kaduna wanda ya samu halartar manyan mutane ciki hadda malaman addini.
A sanarwar da kungiyar ta fitar ranar Laraba, ta sanar da cewa, tana jinjinawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda nada Yazeed Shehu Danfulani shugaban hukumar inshora ta manoma ta kasa, (NAIC).
Kungiyar a sanarwar wadda kakakinta, Mr. Seun Ogunyinka ya ftar tace nadin ya karfafa matasa sannan kuma ‘yan Najeriya da dama sun ji dadi inda suka bayyana Danfulani a matsayin gwarzo wanda aka sanshi da aiki Tukuru.