
Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke sanya ido kan mnakaman nukiliya ta yanke hukuncin cewa Iran ta karya ƙa’ida da aka shimfiɗa kan makaman Nukuliya.
Bayan an kaɗa ƙuri’ar makamai a Vienna, hukumar ta kuma nemi Iran ta yi bayanin yadda aka gano kayan haɗa makaman nukiliya a wasu yankuna da Tehran ba ta bayyana ba.
Daukar sabon matakin zai iya kaiwa ga sabbin takunkuman da aka janyewa ƙasar shekaru 10 da suka gabata.
Da Iran take mayar da martani ta ce, sakamakon hukumar cike yake da siyasa, sannan za ta ci gaba da sarrafa sinadarin Uranium.
Oman ta tabbatar za a koma tattaunawa tsakanin Amurka da Iran game da makaman nukiliyar ranar Lahadi a birnin Muscat.