Friday, December 26
Shadow

Ina jin daɗin ganin jam’iyyun adawa cikin matsala – Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce yana farin ciki da halin rikici da jam’iyyun adawa da dama na ƙasar ke ciki.

Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin jawabin da ya yi na ranar tunawa da dimokuraɗiyya a zauren majalisar dokokin ƙasar da ke Abuja, yau Alhamis.

“Ina jin daɗin ganin jam’iyyun adawa a tagayyare,” kamar yadda shugaban ƙasar ya bayyana a jawabinsa na ranar dimokuraɗiyya.

Tinubu ya ce “ba zan ce ina so na ga kun gyaru ba, ina ma jin dadin ganin ku a haka.

Hakan na zuwa ne yayin da jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar ke ci gaba da karɓar ƴan siyasa masu sauya sheƙa daga jam’iyyun adawa zuwa cikinta.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Shinkafar da aka bamu bata dahu ba, kuma ba nama, Inji daya daga cikin wadanda suka halarci wajan dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya a Legas

Tinubu ya ce jam’iyyar APC ba za ta hana kowa shiga cikinta ba domin yin hakan tauye hakkin al’umma ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *