
Rahotanni daga kasar Iran na cewa, Zanga-zanga ta barke inda mutanen kasar ke neman kasar tasu ta mayar da martani me zafi kan kasar Israyla.
Bidiyo sun bayyana inda aka nuna Iraniyawa maza da mata na kuka suna dauke da hotunan mutanen da aka kashe a kasar.
Masana kimiyyar Nòkìlìyà da manyan sojojin kasar da yawa ne aka kashe.
Lamarin ya zo da ba zata inda kasar iran din bata tabuka wani kokari na kare harin da aka afka mata ba.