Kungiyar kwadago ta NLC ta jaddada matsayinta na cewa sai Gwamnatin tarayya ta biya Naira 250,000 a matsayin mafi karancin Albashi.
Shugaban NLC, Joe Ajaero ne ya bayyana haka a inda yace suna jiran shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dauki mataki kan lamarin.
Gwamnatin tarayya dai tace Naira 62,000 ne zata iya biya a matsayin mafi karancin Albashin.
Saidai Gwamnoni sunce au bazama su iya biyan hakan ba idan dai ba duka kudaden da suke samu bane zasu rika biyan Albashi dashi ba.
Yanzu dai abin jira a gani shine yanda zata kaya.