Friday, December 26
Shadow

Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Allah-Wàdai Ďa Hàrin Isra’ìlà À Jamhuriyar Musulùñci Tà Iŕàñ

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta bayyana damuwa matuka kan rikicin da ke kara kamari tsakanin Jamhuriyar Mùšulunci ta Iran da ķàsar Isra’ila, inda ta yi Allah-wadai da harin farko da Iśŕà’ila ta kai kan Iran, wanda ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin rikici mai haťsari.

Najeriya ta yi kira da a dakatar da harin tare da kira ga bangarorin biyu da su nuna juriya da hakuri don kare zaman lafiya a yankin da ma duniya baki daya. Ta bayyana cewa, ci gaba da mayar da martani tsakanin kasashen biyu zai cigaba da barazana ga rayukan fararen hula da kuma kara tayar da hankalin duniya, ciki har da tabarbarewar tattalin arziki da tsaro.

Karanta Wannan  Gwamnatin Sokoto ta ƙaddamar da tallafin azumi ga masu buƙata ta musamman

A cikin wata sanarwa da kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya fitar daga birnin Abuja a ranar Asabar 14 ga Yuni, 2025, Najeriya ta bayyana cewa tana tsaye tsayin daka kan bin ka’idojin zaman lafiya da amfani da hanyar diflomasiyya wajen magance wannan rikici.

“Najeriya na kira ga kasashen biyu da su zabi tattaunawa maimakon fada. Haka kuma, muna kira ga al’ummar duniya musamman Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da su kara matsa lamba domin ganin an samu saukin lamarin da kuma samar da yanayi na shawarwari masu amfani,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa yaki ba zai iya maye gurbin sulhu ba, sannan mafita mai dorewa tana cikin tattaunawa, mutunta juna da bin dokokin kasa da kasa. Najeriya ta ce a shirye take ta goyi bayan duk wani yunkuri na gaske da zai taimaka wajen rage tashin hankali da tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

Karanta Wannan  Majalisar wakilan Najeriya na son a ƙwace ikon yi wa jam'iyyu rajista daga wurin INEC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *