Mahàifì Ya Dauŕe Ķaŕamiñ Ďansa Da Añkwa Tare Da Kòna Shi Saboda Yana Zuwa Wajen Mahaifiyarsa Da Ya Sake Ta.

Wani mutum mai suna Bala, daga karamar hukumar Illela a jihar Sakkwato, ya daure dansa ƙarami tare da azabtar da shi, bisa zargin cewa yaron yana zuwa wajen mahaifiyarsa, wacce ake kyautata zaton cewa sun rabu da Bala tsawon lokaci da ya wuce.
Wannan lamari ya jawo babban damuwa da alhini, kasancewar irin wannan danyen aiki ya sabawa doka, hankali, da kuma hakkokin yara da iyaye.
Akwai bukatar jami’an tsaro da hukumomin da abin ya shafa su gaggauta daukar matakin kare wannan yaro daga chi gaba da fuskantar irin wannan zalunchi. Dole ne a nemo mafita da maslaha mai dorewa domin inganta rayuwarsa da tabbatar da cewa ya samu kulawa, kariya, da”‘yanchin da kowanne yaro ke da shi a karkashin doka.
Muna kira ga hukumar kare hakkin yara, jami’an “yan sanda, da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa an ɗauki matakin da ya dache, tare da gurfanar da duk masu hannu a wannan aika-aika domin a samu adalci ga yaron da kuma kariya ga sauran yara a cikin al’umma.
Daga Shetteeman Goronyo