
Biyo bayan zaman sulhu da sasanci da ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Ɗanmusa ta jihar Katsina ƴan bindigar sun sako mutanen da suke garkuwa dasu Goma Sha Shidda tare da bada wasu bindigogi dake hannun su.
A ƙoƙarin su na ganin an samu zaman lafiya shuwagabannin sojoji dake jagorancin rundunar jami’an tsaron Operation Fasan Yamma haɗin guiwa da sauran masu ruwa da tsaki sun jagorancin zaman Sasanci a ƙaramar hukumar Dan Musa.
Inda ƙasurguman ƴan bindiga da suka haɗa da Kamulu Buzaru, Manore, Nagwaggo, Lalbi, Alhaji Sani, Dogo Baidu, Dogo Nahalle, da Abdulkadir Black suka aje makaman su bisa raɗin kansu tare da sako waɗanda suka yi garkuwa dasu a ranar 14 June 2025.
Ƴan bindigar sun bayyana cewa sun miƙa wuya kuma dagaske suke akan wannan sasancin, inda makaman da suka bada aka miƙa su ga hukumomin da abin ya rataya a kana su.
Mutanen Goma Sha Shidda da aka sako sun haɗa da Manyan Mata guda Bakwai da ƙananan yara guda Tara sun kuma yi alkawalin cewa yau Lahadi 15 June 2025 zasu sako sauran Mutanen da suke garkuwa dasu.
Sojojin sun bayyana cewa har yanzu suna cigaba da zama yankin tare da bibiyar yadda lamarin zai ɗore, kamar yadda Jaridar Katsina Post ta ruwaito.