
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya taka rawa shi da matarsa, Titi Abubakar a yayin da take bikin cika shekaru 75 da haihuwa.
Atiku yace shekararsu sama da 50 da aure inda ya jinjinawa matar tasa da cewa ta yi hakuri da halinsa.
Atiku yace duka iyayensu biyu basu son aurensu amma a haka suka yi auren da bokai biyu kawai da suka halarta.