
Babban Malamin Shi’a, Sheikh Zakzaky ya bayyana cewa, saboda murna ji yayi kawai hawaye ya zubo masa.
Zakzaky ya bayyana hakane a cikin wani Bidiyo da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta inda yake bayyana murna da martanin da Kasar Iran ta mayarwa da kasar Israyla.
Yaki ya barke tsakanin kasar Israyla da Iran ne bayan da Israylan ta afkawa Iran da zummar cewa tana son hanata mallakar makamin kare dangi.
Mutane da dama ne suka rasu daga kowane bangare.