
Kotu a Jos, babban birnin jihar Filato ta yankewa abokai biyu hukuncin daurin watanni 12 a gidan yari.
Wadanda aka daure din sune, Michael Auta da Gabriel Sunday.
Dukan su dai sun amsa laifinsu.
Kayan da suka sata darajarsu ta kai Naira 488,000.
Mai shari’a, Mrs Shawomi Bokkos ta yanke musu hukuncin daurin watanni 2 a gidan yari ko kuma su biya diyyar Naira 50000.
Sannan ta bukaci kowannen su ya baiwa me shagon Naira 200,000 ko kuma a kara musu wani hukuncin daurin watanni 12.
Dansanda me gabatar da kara, Insp Daniel Damulak ya gabatarwa da kotu cewa wata mata me suna Ms Gift Ernest ranar 17 ga watan Aprilu ya kai musu korafi.
Ta yi zargin wadanda aka kama din sun shiga shagonta inda suka sace mata kayan da suka kai na Naira 488,000.
Yace kuma bayan bincike duka sun amsa laifukan nasu.