
Rahotanni sun ce gwamnatin tarayya na shirin siyo jiragen sama da ake kira da AH-1Z Viper attack helicopters guda 12 daga kasar Amurka.
Shugaban sojojin sama, Air Marshal Hasan Abubakar, ne ya wakilci Najeriya wajan zuwa kasar Amurka dan tattauna maganar siyen jiragen.
Kakakin Hukumar sojin Saman Najeriya, Air Commodore Ehimen Ejodame ne ya fitar da sanarwar inda yace an yi ganawar tsakanin shugaban sojojin Najeriya da kuma wakilan kasar Amurka a birnin San Diego na jihar California.
Yace kuma shugaban sojojin ya kai ziyara masana’antar kera jirgin samma an tattauna yanda za’a kawo shi Najeriya da irin amfanin da za’a yi dashi da kuma irin taimakon da kasar Amurkar zata baiwa Najeriya wajan kula da jiragen.