Friday, December 5
Shadow

Da ya dauki bìndìgàr mahaifinsa dansanda ya harbe mahaifin ya mùtù

Wani abin takaici ya faru a garin Awka, na jihar Anambra inda yaro dan shekaru 10 ya dauki Bindigar mahaifinsa Dansanda, AK47 ya dirka masa harsashi ya mutu.

Mahaifin na da mukamin Inspector ne kuma sunansa Okolie Amechi.

Lamarin ya faru ne a gidan marigayin inda kuma harsashi ya samu dayan dan nasa me suna Emmanuel a hannu.

Rahoton yace yaron na wasa da Bindigar ne inda bisa tsautsai ya harbata, ta samu mahaifin nasa a baya sannan harsashin ya wuce ya samu dayan dansa a hannu.

Kakakin ‘yansandan jihar, SP Tochukwu Ikenga ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an kai gawar mahaifin asibiti inda shi kuma dayan da nasa na can ana bashi kulawa ta musamman.

Karanta Wannan  Sabbin Motocin jigilar man fetur da muka kawo zasu samar da ayyuka 15000>>Dangote

Ya bayyana cewa, hukumar ‘yansandan jihar ta yi alhinin wannan abin da ya faru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *