
Shiga tasharmu ta WhatsApp dan samun labarai: https://whatsapp.com/channel/0029VbA9rBN1SWt61nQZUj1g
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi Allah wadai da yunkurin dukan sa da aka so yi a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar Gombe.
Ya bayyana cewa abin rashin kishin kasa ne kuma abune na rashin da’a.
Sannan yace hakan zai iya dagula lamarin siyasar kasarnan.
Ganduje ya bayyana hakane ta bakin hadiminsa na musamman dake taimaka masa kan wayar da kan mutane, Chief Oliver Okpala a sanarwar da ya fitar ranar Litinin.
Yace irin wannan abin da ya faru a jihar ta Gombe shine ya taba faruwa a zamanin Jamhuriya ta farko wanda ya kai ga yakin basasa.
Ya kara da cewa Ganduje uban kowane, tun bayan da ya zama shugaban jam’iyyar kullun kokarinsa shine hada kan ‘yan jam’iyyar da ci gabanta.
Yace a wajan Taron, Ganduje yayi iya kokarinsa wajan fahimtar da mutanen cewa yankin Arewa maso gabas na da muhimmanci a siyasar Najeriya musamman yanda mataimakin shugaban kasa ya fito daga yankin.
Hakanan kuma Tikitin takarar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Kashim Shettima duk guda dayane.
Yace amma haka suka ki saurarensa suka yi yunkurin dukansa wanda yace hakan ba cin zarafin ganduje bane kadai hadda ma shugabancin jam’iyyar gaba daya.
Saida ya yabawa jami’an tsaro da suka jajice wajan ganin sun baiwa shugaban jam’iyyar kariya har ya shiga motarsa.
Ya kara da cewa, babban abin takaici shine yanda a wajan taron akwai gwamnoni wanda hakan ya kamata ace an samu nutsuwa sosai a wajan amma lamarin ya zama ya baci.
Ya jawo hankalin ‘yan siyasa da su rika nunawa mabiyansu cewa, siyasa ba fada ko zage-zage bace, sulhu ce da tuntuba da bin diddigi.