
Fargaba ta kunno kai a cikin jam’iyyar APC bayan rikicin da ya faru a jihar Gombe wajan taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar daga Arewa maso gabas.
Hatsaniya ta kaure a wajan taron bayan da aka bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin dan takarar APC da yankin zai goyi baya amma ba’a ambaci sunan mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima ba.
Rahotanni sun ce bayan rikicin, wasu wakilai daga jihar sun bayyana cewa, Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar zasu zaba a 2027 idan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bai tafi da Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa ba a zaben shekarar 2027.
Wani daga jihar Adamawa a wajan taron ya bayyana cewa zai koma jam’iyyar PDP muddin aka cire Shettima a matsayin mataimakin shugaban kasa.