Monday, March 24
Shadow

Farashin gangar man fetur a kasuwar Duniya ya fado kasa inda hakan kewa hanyar samun kudin Gwamnatin Najeriya barazana

Farashin gangar man fetur na Bonny Light wanda Najeriya ke sayarwa a kasuwar Duniya ya fadi kasa zuwa Dala $73.53 akan kowace ganga.

A baya, 15 ga watan Janairu ana sayar da gangar man akan dala $84.02 kowace ganga wanda hakan ya nuna an samu asarar dala $10.6 a farashin bayan fadduwarsa.

Hakan zai iya zama barazana ga hanyar samun kudin gwamnatin Najeriya dan aiwatar da kasafin kudin shekarar 2025.

An shirya kasafin kudinne akan kiyasin farashin kowace gangar man fetur din za’a sayar da ita akan dala $75 inda ake tsammanin rika samun gangar man miliyan 2.06 kullun.

Ana tsammanin samun kudin shiga da suka kai Naira Tiriliyan N36.35 wanda kuma kaso 56 na cikin kudin ana tsammanin su fito ne daga hadahadar man fetur.

Karanta Wannan  Karanta Kaji:Sanatoci 3 kacal da suka ciri tuta suka ki amincewa da dokar dakatar da Gwamnan Rivers da shugaba Tinubu yayi

Hakan na nuna cewa farashin kasuwar man a yanzu yayi kasa da kaso 6.6 akan yanda gwamnati ke tsammanin sayar dashi sannan kuma yawan gangar man da ake fitarwa itama ta yi kasa bata kai yanda ake tsammani ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *