Monday, December 16
Shadow

Mulkin Tinubu ya saka ‘yan Najeriya cikin matsananciyar Wahala>>Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, Mulkin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jefa ‘yan Najeriya cikin wahala.

Ya bayyana hakane a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 26 ga watan Mayu.

Ya bayyana cewa, Gwamnatin Tinubu ta dauki matakai 3 wanda 2 dolene amma ba’a daukesu yanda ya kamata ba.

Yace Gwamnatin Tinubu ta dauki matakin cire tallafin man fetur da kuma na dala.

sannan sai kuma shiga lamarin juyin mulkin kasar Nijar.

Yace gyaran tattalin arziki ba’a yinshi dare daya. Yace dolene sai an dage, yace idan aka dauki matakan da suka dace, cikin shekaru 2 Najeriya zata iya daukar saiti.

Karanta Wannan  Ba A Bi Umarnin Da Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Bayar Na Sake Fasalin Naira Ba>>Tsohon Daraktan CBN Ga Kotu

Ya bayar da misalin yanda kamfanin Total Energy suka zagaye Najeriya suka je kasar Angola suka zuba jarin dala biliyan 6.

Obasanjo yace maganar gaskiya dole a fadeta, gwamnatin Tinubu ta kasa daukar matakan saisaita tattalin arzikin Najeriya ta yanda hakan zai jawo hankalin masu zuba jari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *