Tattaunawa na ci gaba da gudana tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago ta NLC da TUC inda ake tsammanin za’a karkare a yau.
Kungiyar tace ta gabatarwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da bukatarta ta a biya Naira 250,000 a matsayin mafi karancin albashi kuma tana jiran ta ji amsa daga gareshi.
Saidai matsayar gwamnati shine biyan Naira 62,000 a matsayin mafi karancin Albashin.
Shuwagabanni kwadagon sun je Geneva, Kasar Switzerland inda suke halartar taro kan kungiyoyin kwadago na Duniya.
Kuma ana tsammanin bayan aun kammala taron, zasu dawo a samu matsaya kan mafi karancin Albashin.