Friday, January 23
Shadow

Amfanin ganyen ayaba

Akwai amfani da yawa da ake yi da ganyen ayaba da suka hada da dafa abinci, gasawa, dama zuba abinci a ciki a ci da kuma yin kwalliya dashi.

Ana amfani da ganyen Ayaba a matsayin kwano a zuba abinci a ciki wanda da zarar an kammala cin abincin sai a yadda. Yawancin an fi yin hakan a kasashen Asia.

Ana kuma yin amfani dashi wajan gasawa ko dafa abinci, Yarbawa kan yi amfani dashi wajan nada Alale a ciki a dafa. Sannan ana nade wasu abubuwa a ciki a gasa.

Hakanan akan yi amfani da ganyen ayaba wajan magance kaikayin fata da kuma ciwo ko bacin ciki.

Karanta Wannan  Ji abinda Mataimakin Gwamnan Kano, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo yayi kan komawar Abba Kabir Yusuf APC da ya jawo masa yabo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *