Friday, December 5
Shadow

Shugaba Tinubu yaki sakawa sabuwar dokar NDLEA hannu, Ji Dalili

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ki sakawa sabuwar dokar NDLEA hannu wadda ‘yan majalisa suka amince da ita.

Shugaban ya aikewa da majalisar tarayya da wasika dake kunshe da dalilansa na kin sakawa sabuwar dokar hannu.

Shugaba Tinubu yace dalilinsa shine sabuwar dokar na kunshe da cewa, idan hukumar ta NDLEA ta kwace kwaya ko kayan laifi, zata iya ajiye ko rike wani sashi na kayan da ta kwace.

Shugaban yace dokar da ake da ita a yanzu ta tanadi cewa ne a saka ko ma wane irin abune aka kwace zuwa asusu na musamman da aka ware dan kula da kayan da aka kwace, kuma bai ga dalilin da zai sa a canja wannan tsari ba.

Karanta Wannan  Hujjojin da kuka kawo na banza da wofi ne, A kul kuka kaiwa Najeriya Khari>>Kasar China ta gargadi Amurka

Yace shugaban kasa ne kawai ke da ikon baiwa duk wata hukuma kudi daga cikin asusun da ake tara kudaden da aka kwace.

Yace tsarin da ake kansa yafi tabbatar da tsarin aiki me kyau da gaskiya da keke da keke ba tare da boye-boye ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *