
Ana zargin ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike da baiwa dansa wani babban fili a Abujan wanda darajarsa ta kai Dala Biliyan $3.6.
Kafar Peoplesgazette ce ta ruwaito labarin inda ta bayyana wasu kafofin da suka tabbatar mata da faruwar hakan wanda aka ce sabawa dokane.
Wike wanda tun watan Augusta na shekarar 2023 yake akan mukamin Ministan Abuja, ya baiwa dan nasa me suna Joaquin Wike filin da ya kai girman Hecta 2000, kamar yanda rahoton ya bayyanar.
Rahoton yace Wike bai bi doka ba wajan baiwa dan nasa wannan makeken fili ba sannan kuma bai ma biya kudaden da ya kamata a biya ba.
Sannan ya baiwa dan nasa Filayen ne a manyan unguwannin Abuja da suka hada da Maitama, Asokoro, Guzape, Bwari, da Gaduwa.
Yawan filayen sun kai Dubu 40.
Wani Hadimin Wiken yace sun bashi shawarar ya tsagaita yawan baiwa ‘ya’yan Nasa filayen da yake amma yace musu yanzu ma ya fara dan yana son ‘ya’yan nasa su zamana sune suka fi kowa yawan filaye a Abuja.
Ya kara da cewa, sun yi aiki da ministoci da yawa amma basu taba ganin irin abinda Wike yake yi ba.
Kafar tace an yi amfani da sunan kamfanin Joaq Farms and Estates Ltd, wajan baiwa ‘ya’yan Wike filayen.