
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa babu gaskiya a maganar da ake yadawa wai ya baiwa dansa filaye a manyan unguwannin Abuja.
Me magana da yawun ministan, Lere Olayinkane ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar ga manema labarai inda yace ko fili daya Wike be baiwa dansa ba.
A baya dai hutudole ya kawo muku rahoton dake cewa kafar Peoplesgazette ta ce ta samu bayanan sirri cewa, Wike ya rabawa ‘ya’yansa filaye a Abuja.
Saidai Wike yace wannan magana karyace da ta fito daga bakin ‘yan jaridar da basu da kwarewa a aikinsu.
Wike yace a ina za’a samu filaye da yawa a Asokoro da Maitama wanda har zai rabawa ‘ya’yansa?
Yace idan kuma jaridar tace gaskiyane rahoton data wallafa to ta kawo takarda me dauke da sunan dan Wike dake nuna alamar cewa ya mallaki filaye.