Friday, December 5
Shadow

Duk wanda ke samun kasa da Naira dubu dari biyu da hamsin a wata talaka ne dan haka ba za’a karbi Haraji a hannunsa ba>>Inji Gwammatin Tinubu

A jiyane shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa dokar canja fasalin Haraji hannu.

Daya daga cikin abinda dokar ta kunsa shine cewa ba za’a karbi Haraji a hannun wadanda ke samun kasa da naira 250,000 a wata ba saboda talakawa ne.

Shugaban kwamitin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kafa dan kula da canja fasalin dokar harajin, Taiwo Oyedele ne ya bayyana hakan.

Ya bayyana hakan a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV bayan da shugaba Tinubu ya sakawa dokar hannu.

Yace a yanzu masu daukar 250,000 a wata ko kasa da haka an sakasu a cikin jerin Talakawa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ganin ana tallar maganin gargajiya da Motar Prado a Kano ya jawo cece-kuce

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *