Friday, December 5
Shadow

Ji bayani dalla-dalla: Shugaba Tinubu ne yacewa Ganduje ya sauka daga shugabancin APC

Shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya sauka daga muƙaminsa bayan kwashe ƙasa da shekara biyu yana jagorancin jam’iyyar.

Wasu majiyoyi daga fadar shugaban Najeriya sun tabbatar wa BBC cewa Ganduje ya ajiye muƙamin ne bayan da fadar shugaban ƙasa ta umarce shi da yin hakan.

“Da gaske ne Ganduje ya sauka tun jiya (Alhamis) aka ba shi umarnin ya rubuta takardar murabus, a yau da safe (juma’a) ya miƙa takardar,” in ji majiyar.

Hakan na zuwa ne bayan wani rudani da aka samu kimanin mako ɗaya da ya gabata a lokacin taron jam’iyyar ta APC na arewa maso gabashin ƙasar.

Karanta Wannan  Gidajen man fetur da 'yan kasuwar man sun tafka Asara bayan da kamfanin mai na kasa, NNPCL ya rage farashin man fetur din inda a yanzu yake sayar dashi da Arha fiye da na Dangote

A lokacin taron, wasu daga cikin ƴan jam’iyyar sun nuna fushi kan rashin bayyana sunan mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima a matsayin wanda zai mara wa Tinubu baya takarar shugaban ƙasa ta shekara ta 2027.

Duk da cewa APC na samun tagomashi a baya-bayan nan ta hanyar karɓar ƴan siyasar da ke sauya sheƙa daga jam’iyyun adawa, masu sanya ido kan lamurran siyasa na ɗora ayar tambaya kan alaƙar shugaban ƙasar da mataimakinsa.

Ganduje ya zama shugaban jam’iyyar APC ne bayan ajiye aikin tsohon shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu, jim kaɗan bayan nasarar jam’iyyar a babban zaɓen shekara ta 2023.

Daga bisani, jam’iyyar ta sanar da naɗin Sanata Abubakar Kyari, wanda shi ne mataimakin shugaban APC shiyyar arewacin ƙasar, a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar.

Karanta Wannan  Farashin Dala a Yau: Naira ta samu tagomashi

Sai dai tun bayan saukar Abdullahi Adamu ne aka yi ta raɗe-raɗin cewar Abdullahi Ganduje, tsohon gwamnan na Kano zai iya maye gurbinsa a matsayin sabon shugaban APC, kafin daga bisani aka tabbatar da naɗin nasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *