
A ranar Juma’a ne shugaban jam’yyara APC na Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya a jiye muƙaminsa na jangorancin jam’iyyar.
Tsohon gwamnan jihar Kanon ya sauka da muƙamin nasa ne bayan shafe kusan shekara biyu riƙe da shugabancin jam’iyyar a matsayin riƙo bayan saukar Sanata Abdullahi Adamu.
Wasu majiyoyi daga fadar shugaban Najeriya sun tabbatar wa BBC cewa Ganduje ya ajiye muƙamin ne bayan da fadar shugaban ƙasa ta umarce shi da yin hakan.
“Da gaske ne Ganduje ya sauka tun ranar Alhamis aka ba shi umarnin ya rubuta takardar murabus, a ranar Juma’a da safe miƙa takardar,” in ji majiyar.
Kusan a iya cewa ya zama al’ada a tsarin siyasar Najeriya kusan duka mutanen da suka jagoranci manyan jam’iyyun ƙasar ba sa wanyewa lafiya da muƙaman nasu.
Wasu daga cikinsu ana dakatar da su, wasu kuma a kore yayin da wasu kuma matsin lamba kan tilasta musu ajiye muƙaman nasu.
Wani abu da masana harkokin siyasa ke ganin son rai ne galibi ke janyo hakan.
Dakta Yakubu Haruna Ja’e Shugaban Sashen Kimiyar Siyasa na Jami’ar Jihar Kaduna, ya ce lamarin ba ya rasa nasaba da babakere da wasu ƴansiyasa ke yi musamman wajen cimma son ransu.
”Su kansu wasu shugabannin jam’iyyar kan nuna son rai, yayin da a gefe guda kuma su ma ƴan siyasa da ke ganin shugabannin jam’iyyar ba za su yi musu abin da suke so na shugabanci ba suke tsangawamarsu tare da sanya su a gaba”, in ji shi.
Abdullahi Adamu: Shugaban jam’iyyar APC na baya-bayan nan da ya sauka daga muƙamin shi ne Sanata Abdullahi Adamu bayan kwashe shekara ɗaya da ‘yan watanni yana jagorantar jam’iyyar.
Tsohon gamnan na jihar Nasarawa ya ajiye muƙamin ne bayan da rashin jituwa tsakaninsa da Shugaba Tinubu.
Mai Mala Buni: A watan Yunin 2020 ne kwamitin gudanarwar APC ya amince da naɗa gwamnan jihar Yobe a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar.
Naɗa Mai Mala na zuwa ne bayan rikicin da jam’iyyar ta shiga a ƙarƙashin jagorancin Adams Oshimole, inda aka ta kai ruwa rana a lokacin har da kotu.
Adams Oshiomole: A watan Yunin 2018 ne jam’iyyar APC ta zaɓi Sanata Adams Oshiomole a matsayin shugabanta a babban taron jam’iyyar da aka gudanar a Abuja babban birnin ƙasar.
To sai dai tsohon gwamnan na jihar Edo ya gamu da matsaloli bayan shekara biyu yana jagorantar jam’iyyar lamarin da tilasta masa sauka daga muƙamin ba tare da ƙarewar wa’adinsa ba.
John Odigie Oyegun: Shi ne mutumin da aka taɓa zaɓa a matsayin jagoran jam’iyyar a 2014 bayan shugaban riƙo na farko.
Toshon gwamnan na jihar Edo ya jagoranci jam’iyyar wajen lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2015.
Sai dai bayan haka ya fara fuskantar suka daga ƴan jam’iyyar, lamarin da ya sa ya haƙura da ƙudirinsa na neman wa’adi na biyu a jam’iyyar.
Tsoffin shugabannin PDP
Ita ma babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta fuskanci irin wannan matsala ta rashin wanyewa lafiya da wasu shugabanninta.
Iyorchia Ayu: Shugaban jam’iyyar na baya-bayan nan da ya fuskanci dakatarwa shi ne Iyorchia Ayu, wanda shugabannin jam’iyyar a matsakin mazaɓarsa suka dakatar.
A watan Oktoban 2021 ne tsohon sanatan na jihar Benue ya zama shugaban jam’iyyar bayan amincewarta.
Sai dai a watan Maris ɗin 2023 ne, aka dakatar da Ayu, lamarin da ya kai ga naɗin shugabanta na yanzu Iliya Damagum.
Uche Secondus: A shekarar 2015 Secondus ya taɓa riƙe kujerar a matsayin riƙo mayan murabus ɗin shugabanta na wancan lokacin.
Sai dai kuma a ranar 10 ga watan Disamban 2017 aka zaɓe shi a matsayin cikakken shugaban jam’iyyar, to amma shi ma ya fuskanci matsalolin da suka kai har zuwa kotu, kafin saukarsa daga kujerar.
Ahmed Makarfi: A shekarar 2016, PDP ta naɗa Makarfi a matsayin shugaban a wani babban taron jam’iyyar da ka gudanar a birnin Fatakwal.
Sai dai jagorancinsa ya gamu da cikas lamarin da ya sa har aka cire tare da naɗa tsohon gwamnan Bornon Ali Modu Sheriff ya jagoranci PDP, kodayake ƙotun ƙolin ƙasar ta yi wani hukuncin da ya mayar da shi kan kujerar daga baya.
Ali Modu Sheriff: Tsohon gwamnan na jihar Borno ya shiga jerin jagororin PDP a lokacin da aka samu wani saɓani a ƙarƙashin jagorancin Maƙarfi, to amma hukuncin Kotun Ƙoli da ya mayar da Maƙarfi ya kawo ƙarshen jagorancinsa a 2017.
Bamanga Tukur: Ya jagorancin jam’iyyar PDP daga watan Maris ɗin 2012 zuwa Janairun 2014.
A lokacin mulkinsa an yi ta samun rikice-rkice tsakanin ƴaƴan jam’iyyar, inda daga ƙarshe tsohon shugaban ƙasar GoodLuck Jonathan ya sanar da murabus ɗin sa a wani a taron kwamitin zartarwar jam’iyyar.
Adamu Mu’azu: Tsohon gwamnman na jihar Bauchi, ya zama shugaban PDP a shekarar 2014, kwanaki kaɗan bayan saukar Bamanga Tukur.
Kamar sauran shugabannin PDP, Mua’zu ya gamu da rikici tsakanin ƴaƴan jam’iyyar musamman bayan shan kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2015, lamarin da ya kai shi ga yanke shawarar sauka daga muƙamin.
Mene ne illar hakan?
Dakta Yakubu Haruna Ja’e ya ce matsalar yawan murabus ko sauke shugabannin jam’iyyun siyasa da ake samu a Najeriya na kawo gagarumin cikas da tsarin ci gaban dimokradiyyar ƙasar.
”Saboda zai zama ana yawan samun rikicin cikin gida a jam’iyyar, saboda mayar da wasu saniyar ware da ake yi, a gefe guda kuma a fifita wasu”, in ji shi.
Masanin siyasar ya ce matsalar za ta hana jam’iyyar gudanar da harkokinta.
”Wannan shugaba ya ɗauko manufofinsa bai gama ba, wannan ya zo kafin ya gama saita komai shi ma tasa matsalar ta taso, to za ka ga a ƙarshen jam’iyyar ce ke cutuwa”, in ji shi.