
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sakawa sabon daftarin doka hannu wanda ya baiwa jihohin Najeriya damar samarwa da rarraba wutar Lantarki a jihohinsu.
Tun a shekarar 2024 daftarin dokar ya wuce amincewar ‘yan majalisa inda ake jiran shugaba Tinubu ya saka hannu amma bai saka ba sai a yau.
Masana sun ce hakan ya canja kula da wutar lantarki a Najeriya wanda a baya yake hannun Gwamnatin tarayya, a yanzu jihohi ne zasu rika samar da wutar.
Hakanan ana tsammanin wannan sabuwar dokar zata jawo masu zuba jari a harkar sannan zata karfafa gasa tsakanin jihohin wanda hakan zai inganta samar da wutar Lantarkin.