
Duk da cewa Aminu Ɗantata ya fi shahara a fannin kasuwanci da kuma tallafa wa jama’a, ya kuma taɓa harkokin siyasa tun daga shekarun 1963.
Ya taɓa zama ɗanmajalisar wakilai a tsohuwar jihar Kaduna na wa’adi ɗaya lokacin Jamhuriya ta Farko daga 1963 zuwa 1966.
Bayan kifar da gwamnatin farar hula ta lokacin ne kuma ya koma Kano, inda gwamnan mulkin soja Audu Bako ya naɗa shi kwamashinan harkokin kasuwanci a 1968.
Ɗantata ya ce yayin da ake shirin shiga Jamhuriya ta Biyu, sai wasu mutane da dama suka fara neman ya tsaya takarar shugaban ƙasa.
Wasu kuma sun nemi ya tsaya takarar gwamnan Kano, cikinsu har da tsohon ɗan gwagwarmaya kuma ɗansiyasa Mallam Aminu Kano. Sai dai bai amince da kiran nasu ba.
“Dalilin da ya sa na ƙi yarda shi ne, a matsayina na ɗankasuwa ina ganin Allah ya riga ya zaɓa min hanyar da zan iya taimakawa wajen cigaban jihata, da ƙasata, da ma al’umma baki ɗaya,” in ji shi cikin hirar ta Trust TV.
“Saboda haka babu wani dalili da zai sa na koma siyasa.”
BBChausa.