
Kungiyar dattawan Arewa ta NEF sun nemi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya ayyana dokar ta baci akan matsalar tsaron Arewa.
Kungiyar dattawan sun kuma yi Allah wadai da kisan sojoji 20 a kananan hukumomin Bangi, Mariga dake Jihar Naija.
A sanarwar da kakakin kungiyar, Prof Abubakar Jiddere ya fitar, yace kisan sojojin alamace ta rashin tsaro a Arewacin Najeriya.
Yace irin wannan hari alamace ta kaddamar da yaki akan Najeriya da ‘yan ta’addar suka yi.