
Rahotanni sun ce tafiyar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi zuwa kasar Saint Lucia da fadar shugaban kasar tace hanyace ta kulla alaka tsakanin kasashen biyu, dabara ce kawai ta neman lafiya da shugaban kasar ya fita yi.
Rahoton yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi amfani da kasar Saint Lucia ne dan neman magani inda maimakon a baya da yake zuwa asibiti, a wannan karin likitocin sa ne za’a dakko su dubashi a kasar.
Rahoton wanda ya fito daga Sahara reporters wadda ita kuma tace ta samoshi ne daga wata majiya me tushe ta kusa da shugaban kasar tace, an yi hakanne dan kaucewa idon ‘yan jarida kada su kwarmata cewa shugaban kasar ya je nema lafiyane.
A baya dai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya je neman lafiya kasashen waje wanda hakan yaci karo da suka daga ‘yan Najeriya.