
Rahotanni na cewa, a watan Yuli ne shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai mayar da gwamnan Rivers, Simi Fubara kan mukaminsa.
Hakanan itama majalisar jihar a wannan watanne ke tsammanin mayar da ita kan aiki.
Hakan na zuwane bayan da aka yi sasanci tsakanin Fubara da Wike.
A ranar 18 ga watan Maris ne dai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara da ‘yan majalisar jihar inda ya bayyana cewa sun samu bayanan sirri musamman game da fasa bututun man fetur a jihar kuma Gwamnan ya kasa magance matsalar.