
Jam’iyyar APC ta saka Naira Miliyan 20 a matsayin kudin sayen fom din takarar sanata sannan ta sa Naira Miliyan 10 a matsayin kudin fom din takarar dan majalisar wakilai a zabukan cike gurbi da ake shirin yi.
Hakan na kunshene a cikin takardar bayanan ya da za’a gudanar da zaben da jam’iyyar ta fitar ta hannun babban sakatarenta, Sulaiman Argungu.
Fom din tsayawa takarar dan majalisar jiha kuwa an sakashi akan Naira Miliyan 2.
Matasa dake tsakanin shekaru 25 zuwa 40 zasu samu ragin kaso 50 cikin 100 na kudin sayen fom din.
Jam’iyyar tace tana sayar da fom din a ofishinta dake Wuse II, Abuja