
Jama’ar gari sun kama wani mutum da aka bayyana a matsayin fasto yana lalata da matar aure turmi da tabarya.
Lamarin ya farune a garin Iguomon dake jihar Edo inda ranar Litinin aka ga Bidiyon lamarin na yawo a kafafen sada zumunta.
Mutanen da suka kama faston dai sun masa tsirara dan kunyatashi.
Zuwa yanzu ba’a kai ga tantance sunan Faston ba.
Hakanan itama matar auren da aka kama an mata tsirara.