Friday, December 5
Shadow

Allahu Akbar: Ji bayanin aikin Alherin da marigayi Dantta yawa kasar Saudiyya da yasa ta amince aka binneshi a Madina

Ko kunsan cewa, Aminu Dantata shine mutum na farko dan Najeriya da ya mutu a wata kasa amma aka mayar dashi kasar Saudiyya aka binne?

Mutane da yawa sun yi mamakin shin wai menene yasa hakan ta faru?

An samu rahotanni da dama dake bayyana dalilin da yasa kasar ta Amince aka mayar da Dantata Madina aka binne duk da cewa ya rasu ne a Abu Dhabi dake kasar UAE.

A wani rahoton an samo cewa, a shekarun baya, dantata na da gida kusa da masallacin Manzon Allah, a wani kaulin kuma kusa da Harami, sai aka tashi fadada masallacin, sai hukumomin Saudiyya suka nemi Dantata yawa gidansa kudi ko nawane zasu saya a rusheshi a fadada masallacin.

Karanta Wannan  An sami rashin fahimta tsakanin ƴan majalisa da ministan tsaron Najeriya kan tsaro

Saidai Dantata yaki sayar da gidan inda yace maimakon haka ya bayar dashi fisabilillahi a rushe a fadada masallacin.

Wannan abu yasa kasar Saudiyya ke ganin kimarsa wanda rahotanni ke cewa dalili kenan da suka bari aka mayar sashi can aka masa sutura.

A wasu rahotannin kuma an ruwaito cewa saboda yana auren balarabiya ‘yar gidan sarautar Saudiyyane.

Koma wannene muna fatan Allah ya jikansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *