
Ministan babban birnin tarayya, Abuja Nyesom Wike ya soki hadakar ‘yan Adawa wanda ya kira da barayin jam’iyya.
Wike yace daga shekarar 1999 zuwa yanzu, sun canja jam’iyya ta kai 10, basu da alkibla, inda ya kara da cewa, rubabbun ‘yan siyasa ne.
Wike yace duk kokarin da shugaba Tinubu ke yi irin wadannan ‘yan siyasa basa gani duk da cewa kowace tasha ka duba Tinubu zaka gani.
Hakan na zuwane yayin da hadakar ‘yan jam’iyyun Adawa suka koma jam’iyyar ADC.