
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tabbatar da rahoton cewa bashi da lafiya.
Ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawunsa, Malam Garba Shehu.
Garba Shehu yace tabbas shugaba Buhari yayi rashin lafiya kuma an kwantar dashi a Kasar Ingila amma a yanzu yana samun sauki.
Ya bayyana hakane ranar Laraba yayin da ake mai tambaya game da ko da gaskene tsohon shugaban kasar bashi da lafiya?
Garba Shehu ya tabbatar da cewa Buhari ya je a duba lafiyarsa a kasar Ingila amma sai ya kwanta rashin lafiya.
Yace amma zuwa yanzu yana samun sauki kuma yana karbar magani.
A lokacin da yake shugaban Najeriya, Shugaba Buhari yayi tafiye-tafiye zuwa kasar Ingila sau da dama dan neman lafiya.