Friday, December 26
Shadow

Amsoshin Tambayoyinku: Wace Irin Rashin Lafiyace ke damun tsohon shugaban kasa, Buhari da karin abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da rashin lafiyar tasa

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[“local”],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari na can a kasar Ingila inda yake jinyar rashin lafiya kamar yanda kakakinsa Garba Shehu ya tabbatar.

Saidai Mutane na ta tambaya da yawa kan wannan lamari, dan haka ga Amsoshinku a kasa.

Yaushe shugaba Buhari ya fara rashin lafiya?

Tin a lokacin bikin cikar kungiyar ECOWAS shekaru 50 ne shugaba Buhari yace ba zai iya halartar taron ba zai je duba lafiyarsa kasar Ingila inda a canne rashin lafiyar ta kamashi.

Wace irin cutace ke damunsa?

Zuwa yanzu babu tabbas kan rashin lafiyar dake damun Shugaba Buhari amma dai a rahoton BBC sun ce wasu na kusa dashi sun ce yana jin jiki.

Karanta Wannan  Na yi dana sanin Shiga Harkar Fim>>Inji Anfara

A wane Asibiti yake kwance?

Ba a bayyana sunan asibitin da tsohon shugaban kasar yake kwance ba amma dai an tabbatar yana kasar Ingila kuma har an kaishi bangaren kulawa ta musamman watau ICU.

Shugaba Buhari ya mutu?

Zuwa yanzu dai babu wata sanarwa data bayyana cewa tsohon shugaban kasar ya mutu, Na kusa dashi dai na cewa yana karbar magani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *