
A jiya ne dai, Nazir Ahmad Sarkin Waka yayi fariyar cewa motarsa tafi ta Rarara tsada inda yace motar tasa zata sayi ta Rarara har sau uku da Canji.
Rarara dai bai kulashi ba, maimakon haka, sai ya wallafa hotunan matasa da ya dauki nauyin aurar dasu.
Rarara ya ce “Yau ldan Allah Ya Kaimu Anjima Ina Gayyatar Dukkan Mutane Daurin Auren ‘Ya’yana Da
Za’ayi a Masallacin Murtala Hausawa Kano
Da Misalin Karfe 2pm Bayan Sallar Juma’ah.”
Tun a jiya dai labarin aurar da mutanen da Rarara zai yi ya bayyana, kuma gashi a yau ya tabbatar dashi.
