
Wani malamin jami’a ya koka da cewa, shigar banza ta yi yawa tsakanin dalibai mata.
Malamin me suna Mr Ishaq Ibrahim na koyarwa ne a jami’ar University of Professional Studies, Accra (UPSA) ta kasar Ghana.
Yayi wannan korafine a yayin hira dashi a gidan talabijin na Metro TV ranar Alhamis, July 3, 2025.
Malamin yace ya kamata a dauki matakin gyara dan kare martabar jami’ar ta UPSA.
Yace akwai sanda yake koyar da dalibai wata daliba data zauna a gabansa saboda gajartar siket din data saka, har dan kamfai dinta yana hangowa.
Yace abin yayi muni a lokacin da cutar Corona Virus ta zo inda yace saboda a kwamfuta ake karatu kuma kowa zai iya shiga aji ta hanyar kiran waya da bidiyo call.
Yace wata dalibar da kayan bacci take shiga ajin, wata kuma ban daki zata shiga tana wanka tana sauraren karatun.
Da yawa dai sun yi kiran a dauki matakin gyara kan lamarin.