Monday, December 16
Shadow

Kaikayin nono ga budurwa: Meke kawo kaikayin nono ga budurwa

Kaikayin nono ga budurwa na iya zuwa saboda wani abu data ci ko kuma haka kawai, ko saboda jinin al’ada, ko bushewar fatar kan nonon da sauransu.

Ga abubuwa 11 dake kawo kaikayin nono ga budurwa:

Tana iya yiyuwa wajan yayi bori ne ko wani kurjine ya fito akan nonon.

Idan kika yi amfani da sabulun da be karbeki ba ko kuma jikinki baya so, zai iya saka kaikai a jiki hadda ma kan nono.

Saka rigar mama wadda ta matse ki na iya sawa kan nonon ki yin kaikai. Idan hakane, ki saka rigar mama wadda bata matseki sosai ba.

Karanta Wannan  Alamomin ciwon damuwa

Tana iya yiyuwa kin yi zufa kika barta ta bushe a jikinki, hakan na iya kawo kaikan kan nono.

Lokacin Al’ada nasa kan nonon mace ya rika kaikai.

Akwai kuma ciwon kansar mama wanda idan kai kayin yayi yawa ya kamata ki je Asibiti.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *