Tuesday, October 15
Shadow

Ranar Litinin za mu kammala kwashe alhazai – NAHCON

Hukumar Alhazan Najeriya wato NAHCON ta ce a ranar Litinin ne za ta kammala kwashe maniyyata zuwa ƙasa mai tsarki, a daidai lokacin da hukumomin Saudiyya suka sanar da rufe filin jirgin Sarki Abdul’aziz da ke Jeddah.

A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara, hukumar ta ce “Jirgin karshe na maniyyata zuwa aikin Hajji na shekarar 2024 zai tashi daga Abuja da sanyin safiyar ranar Litinin, 10 ga watan Yunin 2024, inda zai nufi Madina.”

Ana dai sa ran cewa jirgin zai ɗauki kimanin alhazai 211 daga Zamfara da Sokoto da Kebbi da Bauchi da Abuja da kuma jNeja, tare da rukunin karshe na jami’an aikin Hajji a cikin jirgin na FlyNas.

Karanta Wannan  Kalli Hotunan jami'an tsaron dake samar da tsaro a Dakin Ka'aba wanda suka jawo cece-kuce

Hakan ne ya kawo ƙarshen “jigilar alhazai na bana zuwa Saudiyya inda Aero Contractors za su kammala jigilar Alhazai masu zaman kansu da karfe 2:00 na rana a yau.” In ji hukumar.

Ana kuma sa ran kamfanin Aero Contractors masu jigilar maniyyata masu zaman kansu su kammala jigilar maniyyatan da karfe 2 na rana a ranar 10 ga watan Yunin 2024, kafin rufe filayen jiragen sama na Jeddah da Madina don gudanar da ayyukan jigilar alhazai masu shigowa.

Dangane da kuma shirin komawa Najeriya bayan aikin Hajjin na bana, hukumar ta ce za ta fara ne a ranar 22 ga Yuni, 2024, bisa tsarin waɗanda suka fara shiga su ne za su fara komawa.

Karanta Wannan  Sudais ya buƙaci maniyyata su zama masu biyayya a lokacin aikin hajji

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *