
Matar mataimakin shugaban kasa, Nana Shettima ta bayyana cewa, Aure ba rayuwar jin dadi bace.
Ta bayyana hakane a wajan bikin dan ministan sufuri, Farouk Alkali da amaryarsa, Salaha Abdulaziz.
Nana Shettima itace uwar taro kuma kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya bayyana cewa, a jawabin ta a wajan taron, ta jawo hankalin iyaye su baiwa ‘ya’yansu tarbiyya.
Tace musamman uwa itace ke da kaso me tsoka wajan gyara tarbiyyar ‘ya’ya.
Ta yi kira ga ma’auratan dasu zama masu yawaita addu’a sannan su more kuruciyarsu da rayuwar soyayyarsu, saidai tace rayuwar aure sai da hakuri dan ba rayuwar jin dadi bace.
A karshe ta yiwa ma’auratan fatan Alheri da kuma fata Kiyayewar Allah.