
Kaso 83 na ‘yan Najeriya sun ce basu amince da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba, kuma basu yadda da gaskiyarsa ba.
Wannan ya bayyana ne a sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da wata kungiya me suna API ta shirya.
A kalla mutane 5,465 ne aka tambaya dake da shekaru 15 zuwa sama.
An gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’ar ne da yarukan Pidgin, Hausa, Igbo, and Yoruba
Hakanan ‘yan Najeriya dai sun ce basu amince da bangaren shari’a ba.
An alakanta hakan da matsin tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke fama dashi.